ABNA24 : Balladur ya ce; Bai amince da shiga cikin fadan da bangarorin biyu su ke yi ba, da kuma kai hare-hare a cikin Kigali da sunan kai agaji da ayyukan jin kai.
Faransa tana sha shuka akan rashin amfani da dama da kuma karfin da take da shi na hana kisan kiyashin da aka yi wa kabilar Tutsi a kasar Rawnada, wanda ya ci rayukan mutane 800,000, kamar yadda MDD ta bayyana.
Iyakar abinda sojojin Faransan su ka yi shi ne dauke ‘yan kasashen waje daga Kigali a cikin ‘yan kwanaki kadan.
Wancan kisan kiyashin dai ya faru ne daga watan April zuwa Yuli na shekarar 1994.
342/